Bayanau
Bayanau Bayanau.ogg (help·info) Wannan na nufin kalma ko kalmomin da ke canza ma'anar siffatau ko aikata. Wannan na nufin yana yin ƙarin bayani game da aikatau a cikin jimla . Wato kenan, wannan kalma, ita ce fitilar da take haskaka aikatau a ganshi a fahimce shi kamar yadda za'a kawo misali a kusa.[1]
Misali
gyarawa- Malama tana tafiya a hankali.
- A fusace ya zo nan.
- Shi da yake magana a gigice, ai ba za a fahimci me yake cewa ba.