Lissafi ko kuma nazari Wata dabara ce wadda take taimaka ma dan Adam yin kidaya da sanin yawan abubuwa da kuma sanin tsarin yadda abubuwa suke idan an cenza su ta wata suffar. Ilimi ne na fasaha wanda kuma ake koyawa dalibai a makarantu domin su koyi yadda za su tsare tsare, zane-zane da kuma ƙere-ƙere ta hanya mai sauki. Shi Lissafi ya rabu kashi biyu, akwai lissafi na lambobi, kasafi da ƙidaya wato (haɗawa, ruɓawa, rabawa da kuma fiddawa)wadda ake kira Aljebra. Akwai kuma lissafi na zane-zane, ƙirƙire-ƙirƙire da sauransu da ake kira Geometri. Geometri tana taimakawa wajen sanin suffar abu: wato tsawonsa, fadinsa, girmansa da yawansa. Tana taimaka mana a takaice a cikin fannin gini, ƙira da kuma suffuri. An yin lissafi kafin ayi wani abu domin a san me nene sakomakon abun idan ya faru wanna bangaren na lissafi ana kiransa Kasafi wato "statistics" a turance. A cikin wanna fanni na Kasafi a kan hada gamayyar abubuwa a yi nazari akan sakamakon da za su bayar idan ayi wani abu akan su ta hanyar anfani da alkalamomin da su ke a cikin su.