Shi dai kunun tsamiya wani nou'in abinsha ne na gargajiya wanda hausawa ke amfani dashi kuma sukan hadashi ne da tsamiya da kuma gero wanda wannan kalmar ta samo asali ne ta hanyar tsamiyan da ake hadata dashi, ana sa mishi kayan kamshi irin su citta, kaninfari da sauran su.